1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin juyin mulki a Burundi ya ci tura

May 15, 2015

Mafi yawan jaridun Jamus a wannan mako sun maida hankalinsu kan yunkurin juyin mulki a Burundi, sai kuma sanarwar dake cewa kasar Liberiya yanzu ta fita daga kangin cutar Ebola.

https://p.dw.com/p/1FQHK
Burundi Putschversuch gescheitert Cyrille Ndayirukiye
Hoto: Reuters/J. P. A. Harerimana

((To madallah. Mafi yawan jaridun Jamus a wannan mako sun maida hankalinsu ne kan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Burundi, sai kuma sanarwar dake cewa kasar Liberiya dai yanzu ta fita daga kangin cutar Ebola

Jaridar Süddeutsche Zeitung tace kokarin juyin mulki a kasar Burundi dai ya ci tura. hakan kuwa ya samu ne bayan da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya nuna karfin zuciya, kuma manyan sojojin dake kusa dashi suka ki baiwa wadanda suka so aiwatar da juyin mulkin goyon baya. Ranar Laraba, tsohon shugaban hukumar leken asiri, Godefroid Niyombare yayi jawabi ta gidan rediyo, inda yace ya kayar da gwamnatin Nkurunziza dake mulki, a daidai lokacin da shugaban yake Tanzaniya, inda yake halartar taron koli na kasashen yankin tsakiya da gabashin Afirka, kan yadda za a sami zaman lafiya a kasar ta Burundi, kasar da tayi makonni da dama tana cikin halin zanga-zanga daga yan adawa bayan da shugaba Nkurunziza yace zai tsaya takarar zabe a wa'adi na uku, duk kuwa da ganin cewar kundin tsarin mulkin kasar bai yarda da haka ba. Shekaru 10 da suka wuce aka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da ta maida kwanciyar hankali a Burundi, bayan yakin basasa na shekaru da dama da ya haddasa mutuwar akala mutane 300.000 tsakanin yan kabilar Hutu masu rinjaye da yan Tutsi tsiraru a kasar.

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta duba kasar Liberia, inda tace wannan kasa ta sami nasarar kawo karshen cutar Ebola da ta addabe ta tsawon wani lokaci. Tun karshen watan Maris, ba a sami wani sabon kamuwa da cutar ba, abin da ya maida ita kasa ta farko a jerin wadanda suka yi fama da Ebola da ta warke daga cutar. Jaridar tace wannan nasara kuwa ta samu ne a sakamakon fadakarwa da rigakafi da kuma taimako da ma'aikatan sa-kai suka bayar a yaki da ita. Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a birnin Monroviya a karshen makon jiya cewar Liberiya din tana iya komawa rayuwar da ta saba kafin bullar cutar, ko da shike bai kamata ta sassauta ba a matakan rigakafi. Majalisar tace muddin ba'a shwo kan cutar gaba daya a yankin Afirka ta yamma ba, to kuwa ita ma Liberiya tana bukatar taka tsan-tsan. Kafin ta shawo kan cutar, akalla mutane dubu 10 da 500 ne suka kamu da ita, inda 4700 suka mutu. Sauran kasashen da ake kokarin ganin suma sun fita daga kangin cutar da Ebola a Afirka ta yamma sune Guinea da Saliyo.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi sharhi a game da sabon shugaban jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance, ko kuma DA kamar yada ake kiranta a Afirka Ta Kudu, Mmusi Maimane, wanda bakar fata ne, inda karon farko kenan da aka sami wanda ba farar fata ba a shugabancin jam'iyyar. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace bisa sa ran watan-watarana zai zama shugaban Afirka Ta Kudu, har ma magoya bayan jam'iyyar ta DA sun fara kwatanta Mmusi Maimane a matsayin dan karamin Obama, musamman ganin karancin shekarunsa, wanda bai wuce 34 da haihuwa ba. Maimane ya gaji wannan mukami ne daga Helen Zille farar fata, wadda ake ganin muddin ta ci gaba da shugabancinta, jam'iyar DA ba za ta yi farin jini ga al'ummar bakar fata ba.

Südafrika Mmusi Maimane
Hoto: imago/Gallo Images

A karshe, Jaridar Welt am Sonntag ta duba illoli ne dake tattare da manufofin taimakon raya kasa. Tace kasshe masu arziki da ci gaba masana'antu a ko wace shekara sukan kashe dubban miliyoyi domin baiwa kasashen Afirka taimakon raya kasa, to amma kamaryadda akan ce wai an dade ana ruwa, kasa na shanyewa, tun da a ko wace shekara akan sami karin 'yan Afirka dake barin kasashen su zuwa kasashe na ketare musaman na Turai. Jaridar tace idan har ana bukatar shawo kan wannan kaura da dimbin yan Afirka, to kuwa tilas ne a yi gyara kan yadda ake amfani da taimakon raya kasar. Ministan taimakon raya kasa na Jamus, Gerd Müller yace Afirka nahiya ce dake da muhimmanci a idanun Jamus, saboda damar da take da ita ta samun bunkasa, amma ba kuma za a manta da gaskiyar cewar Afirka din nahiya ce dake fama da matsaloli da wahaloli har yanzu ba.

Da wannan sharhi na jaridar Welt am Sonntag zamu dakata a shirin, Abdurrahman gareka.))