1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin Jamus kan tsarin G20 a Afirka

Mariam Muhammad Sissy
December 12, 2017

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier na ziyarar wasu kasashen Yammancin Afirka inda ya fara yada zango a Accra kasar Ghana domin kulla yarjejeniyar da aka sani da "G20 Africa Compact" wace kasar Jamus ta assasa.

https://p.dw.com/p/2pF7n
Bundespräsident Steinmeier in Ghana
Hoto: DW/Isaac Kaledzi

Tawagar shugaban kasar ta Jamus Frank –Walter Steinmeier sun hada da kwararru a fanin kasuwanci da fannin zuba jari da kuma masana a ilimin horrar da kananan sana’oi. Ziyarar ta fara da wani taro na musamman, inda shugaban kasar ta Jamus ya sadu da wakilai daga kamfanoni kasar Ghana, domin jin ra’ayoyin da kuma irin kalubalen da suke fuskanta a sana’o'insu. A lokacin da shugaban kasar TA jamus ya gana da takwaransa na kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya yi jawabi kamar hakan

" Ina mai imani ba tare da wani shaku ba, dangane da alkawarin da shugaban Nana Akufo-Addo ya yi wa al’umman kasa cewa, zai yi shimfida mai  ban sha’awa, kuma mai kyau a kasar Ghana, wace za ta zama sanadiyar sha’awar zuba jari, sai kuma daya daga abin da kuma ke daukar hankali a kasar Jamus shi ne, wace irin gudumawa za ta bai wa kasashe kamar Ghana, domin rage ko hana matasan ta kwarara zuwa kasashen waje"

Ghana - Bundespräsident Steinmeier
Shugaba Steinmeier a tsakiyan wasu 'yan matan GhanaHoto: picture-alliance/dpa/B. v. Jutrczenka

Kasar Jamus a wannan ziyarar ta Steinmeier, ta kulla wata yarjejeniya da kudin sa ya kama Euro million 100 a fannin ayyukan sabunta makamashi daga rana da iska, bugu da kari kuma da horar wa ga matasa masu sha’awar ayyukan hannu. A jawabin maraba shugaban kasa Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya jinjina wa gwamnatin Jamus.

"Duk wanda ya yi bibiyar kwarewan kasar Jamus da kuma tattalin arzikin ta, ya san tafi bada fifiko a fanin ayyukan makamashi, habakar kananan sana’oi. A Ghana kuma babban matsalar mu ke nan, na yi imani Ghana ta ci amfanin wannan kawance kuma mu yi koyi daga kwararru"

Su kuwa wadanda aka yi domin su, kamar Alhaji Razak Khailan,darakta mai kula da sadarwa na Nano Energy cewa yake "Muna masu farin ciki da karban wannan arziki da hannu biyu-biyu musamman ma a fanin makamashi ta amfani da rana, muna godiya ga Allah da shigowan wannan tawaga Jamus a nan kasar, domin zuba jari a fannin ayyukan makamashi".