1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwararru na WHO na kokarin hana yaduwar Ebola

Salissou Boukari MNA
May 20, 2018

Ma'aikatar lafiyar a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango ta dauki matakai na kawo karshen yaduwar cutar Ebola da ta bulla tun daga ranar takwas ga watan Mayu a yankin Arewa maso Yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/2y2gY
Ebola-Ausbruch im Kongo
Hoto: Reuters/J. R. N'Kengo

Tuni aka kebe wadanda suka kamu da cutar kuma ake kula da su a babban asibitin Wangata da ke tsakiyar birnin Mbandanka, birnin da ke da jama'ar da yawanta ya kai mutum miliyan daya da dubu dari biyu. A cewar Docta Hilaire Manzibe, babban daraktan wannan asibitin da ake kula da 'yan malatin na Ebola, lalle ba za su iya bayyana adadin wadanda suka kamu da cutar da a yanzu aka killacesu ba, amma suna sanar da cewa an samu wadanda suka mutu, kuma sauran wadanda ake kula da su na da alamun samun sauki.

Sai dai babban likitan ya ce abin damuwar ma a nan shi ne yana tune a ranar daya ga watan Mayu an kawo wani mai zazzabi kuma yana amai, amma danginsa suka nemi da a ba su shi su yi masa na gargajiya.

A halin yanzu dai duk wasu da suka yi mu'amula da masu dauke da cutar an killacesu har na tsawon lokaci.

Tuni dai hukumar lafiya ta duniya WHO ta aike da wata tawagar kwararru guda 35 da  suka kware wajen allurar rigakafi, kuma 16 daga cikinsu sun taka rawar gani a lokacin yaki da annobar cutar ta Ebola da aka fuskanta a wasu kasashen yammacin Afirka.