Kokarin ceto kasar Girka | Labarai | DW | 24.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin ceto kasar Girka

Ministocin kasashen da ke amfani da kudin Euro, za su sake zama a birnin Brussels a kokarin cimma yarjejeniyar fitar da kasar ta Girka daga fadawa ga matsalar laifin biyan bashi.

Wannan dai shi ne karo na uku a cikin mako guda da ministocin kudin za su zauna kan batun kasar ta Girka kafin babban taron koli na kungiyar Tarayyar Turai da zai gudana a gobe da jibi, taron kuma da zai tabo wannan batu na kasar Girka. Daga nashi bangare ministan kudin kasar ta Girka Alexis Tsipras, zai gana da shugabannin Tarayyar Turai, da na babban bankin Turai, da kuma na Asusun bada lamuni na duniya.