Kokari kan yaki da Ebola a Kwango | Labarai | DW | 09.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokari kan yaki da Ebola a Kwango

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Kwango ya yaba yadda hukumomi, da ma kungiyoyin kasa da kasa ke taka rawar gani, wajen yaki da cutar Ebola a wannan kasa.

Cikin wata sanarwa da ofishin nasa ya fitar, bayan kammala wata ziyara da ya kai a yankin Boende inda ake fama da wannan cutar da ke a nisan kilo-mita 800 a arewa maso gabacin Kinshasa, wakilin na Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Kongo Martin Kobler, ya ce idan da duk masu hannu cikin lamarin da ma mutanen karkara za su ba da himma tare da bin umarni kamar yadda ake bukata, to da nan da 'yan makonni masu zuwa za a iya shayo kan wannan cuta a wannan yanki.

A cewa hukumar Lafiya ta duniya WHO da ma gwamnatin ta Kwango, cutar ta Ebola a wannan kasa dai ta sha bamban da wadda yanzu haka ke addabar yankin yammacin Afirka, inda ta yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 3,900.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleman Babayo