Kisan kiyashi kan Yazidawa | Labarai | DW | 16.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kisan kiyashi kan Yazidawa

Masu gudanar da bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun ce 'yan kungiyar nan ta IS na yin kishan kiyashi kan Yazidawa a kasar Iraki da kuma Siriya.

A wani rahoto da suka fidda, masu bincike suka ce tun cikin shekarar 2014 ne 'yan IS suka fara wannan ta'annati wanda kuma in ba hankali aka yi za su shafe Yazidawan daga doron kasa. Rahoton mai shafi 40 ya bukaci kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya tashi tsaye wajen yin dukannin abin da ya dace don kawo karshen wannan lamari kafin ya yi lalacewar da ba za a iya gyarawa ba.

Wadandan suka jagoranci wannan bincike sun kuma yi kira ga kasashen duniya da ke da karfin fada a ji su ceto mata da kananan yara kimanin dubu 3 da 200 wanda 'yan kungiyar ta IS ke rie da kana mika wanda ke da hannu kan wannan lamari ga kotun ICC.