Kisan haunin kungiyar IS Jihadi John | Labarai | DW | 13.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kisan haunin kungiyar IS Jihadi John

Firaministan Birtaniya David Cameron ya ce harin da Amirka ta kai kan 'yan ta'addan IS da ake zaton ya hallaka haunin kungiyar Mohammed Emwazi da aka fi sani da Jihadi John hari ne na kare kai.

Haunin kungiyar ta'addan IS Jihadi John

Haunin kungiyar ta'addan IS Jihadi John

Cameron ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai, ko da yake ya ce kawo yanzu babu tabbacin cewa an kashe shin. Ya kara da cewa harin da aka kai na musamman a kan Mohammed Emwazi kokari ne na hadin gwiwa tsakanin Amirka da Birtaniya. A nasa bangaren da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Amirka na Associate Presss, tsohon Firaministan Birtaniya kuma tsohon jakadan bangarori hudu da ke kokarin sasanta rikicin yankin Gabas ta Tsakiya Tony Blair cewa ya yi:

"In har rahoton gaskiya ne cewa an kashe ‘yan kungiyar IS masu yawa a harin, mutanen da ke cin zarafi da aikata ta'addanci da kisa a kan al'umma abu ne mai muhimmanci mu yake su mu nuna musu cewa za mu yi maganinsu da karfin tsiya. A ganina ya kamata Birtaniya ta shiga cikin yakin da ake da wannan kungiyar gadan-gadan, mu taka rawa tare da Amirka da sauran abokanmu."

Emwazi da ya kasance dan asalin kasar Birtaniya ya fito a fafayen bidiyon kungiyar IS sau da dama yana yanke akwunan mutanen da suka kama a matsayin fursunan yaki, ciki kuwa har da 'yan kasashen Birtaniyan da Amirka.