1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kisan Gillar Isra’ila akan Shugaban Kungiyar Hamas Ahmad Rantisi

April 19, 2004

A ranar asabar da ta wuce jiragen saman yakin Isra'ila masu saukar ungulu suka kai farmaki tare da kisan shugaban kungiyar Hamas ta Palasdinawa a Gaza

https://p.dw.com/p/Bvka
Dr. Abdel-Aziz Rantisi lokacin wata lacca a jami'ar Gaza
Dr. Abdel-Aziz Rantisi lokacin wata lacca a jami'ar GazaHoto: AP

A dai misalin makonni uku da suka wuce marigayi Ahmad Rantisi yayi barazanar kai farmaki kan Isra’ila daga kowace fuska. Amma wannan barazanar ba ta tabbata ba saboda tsautsayin harin Isra’ilar ya rutsa da shi daidai da magabacinsa Sheikh Ahmad Yassin. Jiragen saman yakin Isra’ila masu saukar ungulu sun kai hari tare da aiwatar da kisan gilla akansa a bainar jama’a. Tare da kisan gillar da Isra’ilar ta yi wa Isma’il Abu Shanab cikin watan agustan da ya wuce, kungiyar Hamas tayi asarar gaggan shuagabanninta guda uku a cikin dan gajeren lokaci. Kuma ko da yake kungiyar ta nada sabon shugabanta, amma fa sannu a hankali al’amura sun fara kai mata iya wuya. To sai kuma hakan ba ya nufin rushewar wannan kungiya, wacce ba ta ga maciji da Isra’ila, bisa sabanin yadda kasar ta Yahudawa take ikirari. Ita dai Isra’ila tayi imani ne cewar wannan mataki na kashe-kashen gilla tamkar wata nasara ce a yakin da ta ce tana yi da ‚yan ta’adda tana mai sako-sako da fushin dake dada yaduwa ba ma a zukatan magoya bayan kungiyar Hamas kadai ba, har da sauran al’umar Palasdinawa da na kasashen Larabawa baki daya. Ita Isra’ila gani take yi cewar tana iya cin karenta babu ba babbaka ko da kuwa za a ci gaba ne da yi mata tofin Allah tsine da kuma mayar da ita saniyar ware. A hakika idan za a yi zance na gaskiya Isra’ila ba zata iya jure irin wannan ci gaba ba, kuma bai kamata goyan bayan da ta samu dagha shugaba Bush na Amurka a baya-bayan nan ya yaudare ta ta jefa kanta da kanta cikin mawuyacin hali na kaka-nika-yi ba. Kowace kasa, kowace al’uma a wannan duniya tamu na bukatar kawaye da abokan hulda, ba zata iya dogara akan wata kawa daya kwal ba kome goyan bayan da zata samu daga gareta, ko da kuwa wannan kawar wata babbar daula ce kamar Amurka. Mai yiwuwa ya zama kuskure idan an danganta matakin kisan gillar akan Rantisi da goyan bayan da Isra’ila ta samu daga shugaba Bush baya-bayan nan, ta la’akari da gaskiyar cewa matakan kisan gillar wani bangare ne na manufofin kasar Isra’ilar tun bayan kafuwarta misalin shekaru 56 da suka wuce. ‚Yan kudumbalar Isra’ila sun sha farautar shuagabannin PLO da aiwatar da kisan gilla kansu a sassa dabam-dabam kama daga Beirut zuwa Cyprus ko Tunesiya. Dukkan shuagabannin Isra’ila ke da alhakin wadannan kashe-kashe na gilla, ba kawai Sharon ba. Amma ba wadannan kashe-kashe ba su tsinana kome ba. Rikici na ci gaba ya ki ci ya ki cinyewa kuma murna ta koma ciki a game da fatan zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wannan abu ne da Sharon ke da cikakkiyar masaniya game da shi. A saboda haka kisan gillar da aka yi wa Rantisi ba ya da nufin lafar da kurar rikici a yankin Gaza. Manufar Sharon a game da umarnin kisan da ya bayar shi ne domin ya nuna wa masu sukan lamirinsa cewar shirinsa na janyewa daga Gaza ba saboda gazawa ba ne kuma baya ma’anar sauya alkiblar siyasarsa. A takaice kisan gillar akan Rantisi wani mataki ne na ramuwa da Sharon ya dauka domin cimma manufofinsa na siyasa a cikin gida, lamarin da wajibi ne duniya tayi Allah waddai da shi ita kuma Isra’ila ta rungumi duk wata kaddarar da zata biyo baya.