Kisan Fararen hula a garin Baga | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 02.05.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Kisan Fararen hula a garin Baga

Duniya ta kaɗu bisa kisan fararen hula da aka yi a birnin Baga dake jahar Borno a Tarayyar Najeriya

Autor: Ubale Musa (Korr DW).in Abuja, Nigeria Below are the pictures of the arrival of the security meeting PIC FROM LEFT: CHIEF OF DEFENCE STAFF, ADMIRAL OLA IBRAHIM; CHIEF OF ARMY STAFF, LT.-GEN AZUBUIKE IHEJIRIKA AND CHIEF OF DEFENCE INTELLIGENCE, MAJOR-GEN. SANI AUDU ARRIVING FOR A MEETING AT THE PRESIDENTIAL VILLA ABUJA ON THURSDAY (4/3/13)

Manyan hafsoshin sojan Najeriya

A shahunan jaridun na Jamus kan nahiyar Afirka za mu faro ne da batun kisan fararen hula da aka yi a garin Baga dake jahar Borno, wannan labarin ya ɗauki hankalin jaridun Jamus da yawa. Jaridar Neue Zürcher Zeitung, ta yi tsukaci kamar haka "Mummunan zubar da jini bisa martanin sojojin Najeriya". Ta ci gaba da cewa, bayan mummunar musayar wuta tsakanin yan ƙungiyar Boko Haram da sojojin Najeriya, a wani ƙauyen da ke da ma sunta wato garin Baga dake arewa masu gabacin Najeriya, kimanin mutane 200 suka mutu. Jaridar tace koda yake an yi wannan munnan zubar da jini tun ranar Juma'a da ta gabata, amma sai ranar Lahdi labarin ya fito a kafafen yaɗa labarai.

In this image shot with a mobile phone, a young girl stands amid the burned ruins of Baga, Nigeria, on Sunday, April 21, 2013. Fighting between Nigeria's military and Islamic extremists killed at least 185 people in a fishing community in the nation's far northeast, officials said Sunday, an attack that saw insurgents fire rocket-propelled grenades and soldiers spray machine-gun fire into neighborhoods filled with civilians.(AP Photo/Haruna Umar) pixel

Yadda wani ɓangaren Baga ya zama bayan harin

Jaridar ta ƙara da cewa wani shaidun ganin ido ya fadawa manema labari cewa. Yan ƙungiyar Boko Haram da ke ɗauke da manyan bindigogi suka laɓe a wata anguwa, su kuwa rundunar hadin gwiwa na sojoji da yan sandan Najeriya, suka kewaye ɗaukacin anguwar suka yi ta bude wuta. a faɗar jaridar wannan fada na Baga shine ya fi zubar da jini a lokaci guda tun fara rikicin ƙungiyar Boko Haram shekaru huɗu da suka gabata, kuma akasari fafaren hulanen suka mutu a gumurzun da aka yi.

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, waiye ta yi kan Faransawan da aka sako, bayan da suka yi makwanni a hannun ƙungiyar Boko Haram. Jaridar ta ce shugaba Paul Biya na Kamarun da takwaransa na ƙasar Faransa wato Francois Holland, su suka fara tabbatar da labarin, inda suka ce mutanen duk sun samu yancin kansu ba rauni, babu kuma wanda ke fama da rashin lafiya. Dama dai ƙungiyar Boko Haram ce ta sace mutanen a kan iyakar Najeriya da Kamaru. Daga cikin wadanda aka sacen akwai yara hudu yan shekaru huɗu da kuma shekaru 12. Dukkannin ƙasashen Kamarun da Faransa dai sun musanta cewa ko sun bada kodin fansa kan a sako mutanen. Abinda kawai shugaba Paul Biya ya faɗawa duniya shine, an samu nasar sako Faransawan bisa tallafin jami'an tsaron Najeriya dana Faransa da kamarun.

CROSS SECTION OF MEMBERS OF THE COMMITTEE ON DIALOGUE AND PEACEFUL RESOLUTION OF SECURITY CHALLENGES IN THE NORTH DURING THEIR INAUGURATION AT THE PRESIDENTIAL VILLA ABUJA ON WEDNESDAY (24/4/13).

Kwamitin da aka nada don sasantawa da kungiyar Boko Haram

Jaridar Süddeutscher Zeitung ta leƙa ƙasar Mali, inda tace batun da aka jima ana anbatonsa wato na horar da jami'an tsaron Mali wanda dakarun Tarayyar Turai suka dauki nauyin gudanarwa, daga ƙarshe dai an fara. Horar da sojan Mali wanda dakarun ƙasashen EU ƙarƙashin ƙasar Jamus za su yi, yana gudana ne a ƙauyen Koulikoro, wanda ke gefen Bamako babban birninƙasar ta Mali. Manufar bada horon dai shine, a samar da rundunar sojan ƙasar Mali wanda za ta iya gudanar da harkar tsaron ƙasar bayan ficewar dakarun ƙasashen waje.

Jaridar Die Zeit kuwa ta duba yadda harkar aikin jarida yake a ƙasar Somalaiya. Tana mai cewa, aikin jarida a ƙasar Somaliya yana da mummunan hatsari, ko da yake kuma barin aikin jarida a ƙasar, shine mafi muni. In babu wanda ka iya aiko abunda ke faruwa a ƙasar. Jaridar ta yi hira da wani ɗan ƙasar ta Somaliya Abdulla Ahmed Mumin, wanda yace tun yana ɗan ƙaramin yaro yake sha'awar aikin jarida. Bayan da Abdul ya girma ya shiga aikin jarida inda yanzu ya yi shekaru 13 yana gudanar da aiki neman labarai. Abdul yace yana rubutu kan cin hanci, da kuma yaƙin ƙasar.

Kashim Shettima, gwamnan jihar Borno Usman Shehu, 15.06.2011, Maiduguri / Nigeria

Kashim Shettima, gwamnan jihar Borno

A makwannin da suka gabata dan jaridar ya ga abun firgita. Inda yan ƙungiyar Al-Shabab suka kai wani mummunan hari a kutun ƙasar dake birnin Mogadishu, aƙalla mutane 32 biyu suka mutu wasu kimanin 67 suka jikkata. Wannan shine hari mafi muni da Alshabab ta kai tun daga shekara ta 2011. Ɗan jaridan yace yana daga cikin yan jarida dake bakin kotun a lokacin da aka kai wannan mummunan harin. Ƙungiyar kare haƙƙin yan jarida ta Reporters Without Borders, tace Somaliya itace ƙasa mafi hatsari bisa aikin jarida baya ga ƙasar Siriya dake fama da yaƙin basasa. Aƙalla yan jarida 18 aka hallaka yayinda wasu 28 suka jikkata bisa hare haren da ake kaiwa manema labar a ƙasar ta Somaliya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Zainab Mohammed Abubakar