Kisan dakarun wanzar da zaman lafiya a Mali | Labarai | DW | 03.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kisan dakarun wanzar da zaman lafiya a Mali

Rahotannin daga Mali na cewar an hallaka wasu dakaru na Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar bayan da aka yi wa jerin gwanon motocin kofar rago.

Mai magana da yawun dakarun na wanzar da zaman lafiya a Mali din Olivier Salgado ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar jami'an nasu da aka kashe sun kai tara kuma dukanninsu 'yan Jamhuriyar Nijar ne.

Mr. Salgado ya ce wasu mahara ne a kan babura dauke da manyan makamai suka yi kisan tsakanin garuruwa Menaka da Ansong da ke arewa maso gabashin kasar ta Mali. Wannan dai shi ne hari mafi muni da dakarun suka fuskanta a kasar a baya-bayan nan.