Kisa mafi muni a tarihin Boko Haram | Labarai | DW | 09.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kisa mafi muni a tarihin Boko Haram

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta bayyana harin da Boko Haram ta kai a garin Baga a jihar Borno da cewa shi ne mafi muni a tarihin kungiyar,

Masu tserewa daga garin na Baga suka ce darururuwan mutane da ba za su kirgu ba sun kwanta dama a harin, musamman ma kananan yara da mata da tsofaffin da ba zasu iya gudu ba. kungiyar ta Boko Haram ta kwaci sansanin soja da ke kusa da iyakar Najeriya da hCadi, bayan da mayakan suka shiga garin a ranar uku ga watan Janairu su na harba makaman roka da gurneti.

Rahoton da kungiyar ta Amnesty ta fitar a ranar Jumma'a, ya nunar da cewa kusan garin an konesh: Sannan kusan mutane 2,000 an kashe, wani abu da ke nuna yadda hare-haren kungiyar ke ci gaba da lakume rayukan fararen hula.

Shekaru biyar na ayyukan Boko Haram yayi sanadin kisan sama da mutane dubu goma a bara kamar yadda wata cibiya mai lura da huldodin kasa da kasa a birnin Washington ta bayyana.