1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kirsimeti: Matakan magance kai hare-hare a Afirka

Yusuf Bala/ASDecember 24, 2015

Hukumomi a wasu kasashen Afirka sun dauki matakai na kare aukuwar hare-haren kunar bakin wake yayin bukukuwan Kirsimeti.

https://p.dw.com/p/1HTQN
Katholische Kirche in Juba
Hoto: Getty Images/AFP/Trevor Snapp

Kasashen Afirka da ke fuskantar kalubalen tsaro sun fidda matakai da suke ganin za su taimaka wajen ganin ba a fuskanci kai hare-hare ga wuraren ibada da kuma inda ake gudanar da shagulgula lokacin Kirsimeti ba. Najeriya dai na daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen daukar matakai na ganin bikin na bana ya gudana ba tare da fuskantar kalubale na tsaro ba.

A lokuta irin wannan dai a kan jibge jami'an tsaro cikin shirin ko ta kwana yayin da 'yan shekarun da suka gabata matasa mabiya addinin Islama suka yi gadin wuraren ibada na Kiristoci don karesu da kai farmaki na 'yan ta'adda. 'Yan kasar dai a wannan lokacin sun bukaci gwamnati da ta rubanya irin matakan tsaon da ta ke dauka da nufin ganin komai ya wakan lami lafiya.

Can a Jamhuriyar Kamaru wakilinmu Adamou Maimota ya rawaito mana cewar jama'a na cikin fargaba ta irin matsalar ka je ta koma duba da yanayin tsaro da kasar da makotanta ke ciki. Wannan ne ma ya sanya gwamnati ta dauki mataki na hana yara wasanni da kayan wasa da suka hada da ababan fashewa da bindigogi na wasa duka dai da nufin tabbatar da tsaro.

Hukumomi a Kamaru din dai suka ce sun dauki wannan mataki ne duba da yadda 'yan kungiyar Boko Haram ke cigaba da kai jerin hare-hare a wasu sassan kasar. Wannan lamari dai bai yi wa yara dadi ba, haka ma abin ya ke ga wanda ke sayar da bindigogin wasa na yara inda a wasu wuraren kasuwarsu ta ja baya ko da ya ke a wasu sassan kasar abin ba haka ya ke ba don mutane na cigaba da sayan bindigogin na wasa da nufin baiwa yara a matsayin kyauta.

Can a Jamhuriyar Nijar ma dai hukumomi sun dau mataki na ganin lamura sun gudana lami lafiya a wannan lokaci na bukuwan na Kirsimite kasancewar kasar kamar takwarorinta na Najeriya da Kamaru, ta na fuskantar kalubale na rikicin da Boko Haram. A gefe guda mabiyan na addinin Krista na gudanar da shagulgulan ne a bana tare da juyayin abin da ya faru a farkon wannan shekarar inda aka kona wuraren ibadar su da gidaje kana kawo yanzun ma wasu majami'un na Kiristocin ba'a kammala aikin sake gina su ba.

Südafrika Weihnachten in Afrika Flash-Galerie
Hoto: AP
Bildergalerie Weihnachten 2014 FOTOLIA
Hoto: Fotolia/Africa Studio