Kirsimeti a New York ya zo da bala′i | Labarai | DW | 25.12.2012
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kirsimeti a New York ya zo da bala'i

Yayinda ake bukukuwan kirsimeti a fadin duniya, wani ba'Amirke ya cinnawa gidansu wuta kana ya harbe mutane biyu ya raunata wasu

A fire burns on Lake Road after a suspect shot four firefighters responding to the blaze in Webster, New York, December 24, 2012. At least two upstate New York firefighters were shot and killed and two wounded on Monday at the scene of an early morning house fire in a suburb of Rochester, according to local news reports. REUTERS/WHEC/Christine VanTimmeren/Handout (UNITED STATES - Tags: CRIME LAW) NO SALES. NO ARCHIVES. FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS

Gidan da ya kama da wuta a Amirka

A jahar New York dake kasar Amirka wani mutumin da ya taba zaman gidan yari ya cinna wuta a gidansu, kana ya labe ya harbi masu wadanda suka zo kashe gobarar biyu kana raunata wasu biyun, kafin daga bisani ya juya bakin bindigar ya harbi kansa. Mutumin dai a fadar yan sanda ya yi zaman gidan yari na shekaru 17, bayan kisan kakarsa da ya yi, kana an yi imanin cewa kanwarsa na cikin dakin da cinnawa wutar.

A gefe guda Kiristoci a fadin na gudanar da bikin ranar Kirsimeti. A fadar Vatikan Paparoma Benedict na16 ya gudanar da addu'o'i a tsakiyan dare, inda ya yi kiran a samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, kana yace kamata ya yi mutane su rungumi son Allah a zukatansu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Saleh Umar Saleh

 • Kwanan wata 25.12.2012
 • Mawallafi Usman Shehu
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/178hf
 • Kwanan wata 25.12.2012
 • Mawallafi Usman Shehu
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/178hf