Kiraye-kirayen kwantar da hankali a Nijar | Labarai | DW | 17.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kiraye-kirayen kwantar da hankali a Nijar

Wasu malaman Islama na Nijar sun yi amfani da kafofin sadarwa wajen yi kira ga masu zanga-zangar da su daina kone-kone saboda ya saba wa koyarwar addininsu.

Shugabannin addini na Jamhuriyar Nijar sun yi kira ga 'yan kasar da su kawo karshen fashe-fashe da kone-konen da suke yi a wasu biranen kasar, bayan hoton Annabi Muhammad SAW da jaridar barkwanci ta kasar Faransa wato Charlie Hebdo ta sake wallafawa a ranar Laraba da ta gabata. Sama da limamai da kuma wasu Ulama 20 ne suka yi amfani da kafar talabijin a birnin Yamai wajen bayyana wa masu zanga-zanga cewar Islama ba ta amince da rusa wuraren ibada na mabiya addinin Kirista kamar yadda suke yi ba.

Wannan jan kunnen ya biyo bayan da jami'an 'yan sanda a Yamai babban birnin kasar Nijar suka yi amfani da borkono mai sa hawaye wajen tarwatsa taruruwa da aka yi a harabar babban masallaci Jumma'a da niyar gudanar jerin gwano. Lamarin da ya haddasa tashin hankali da kone-konen tayoyi inda aka kona motocin 'yan sanda guda biyu, tare da kona Coci-Coci da dama.

A birnin Maradi ma dai wasu matasa sun kona tayoyi a wasu unguwanni. sai dai jami'an tsaro da ke sintiri cikin birnin sun tarwatsa su. Tuni dai Jakadan kasar Faransa a Jamhuriyar Nijar ya yi kira ga 'yan asalin kasarsa da su yi taka tsan-tsan.