Kiran Hamas ga Fatah a kan kafa gwamnati | Labarai | DW | 19.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kiran Hamas ga Fatah a kan kafa gwamnati

Ƙungiyar Hamas ta Haniyeh ta buƙaci ƙungiyar Fatah ta Abbas da su kafa gwamnati ɗaya tilo da za ta ciyar da Palesɗinu gaba.

Ƙungiyar Hamas wacce ke da tsatsaura ra'ayi a kan fafutukar da ta ke yi na neman 'yancin Palasɗinu ta yi kira ga ƙungiyar Fatah ta Mahmoud Abbas da cewar lokaci yayi da za su haɗa kai domin kafa gwamnati ɗaya. Lokacin da ya ke magana a kan batun firaminstan Hamas da ke riƙe da ɓangaran Gaza Ismail Haniyeh ya ce halin da muke ciki ba ya ba mu damar ci gaba da zaman cikin ɓaraka. Ya ce ya kamata mu kafa gwamnati ɗaya majalisa ɗaya kana mu zaɓi shugaban ƙasa ɗaya.

Bayan dai nasara da ƙungiyar Hamas ta samu a zaɓen da aka gudanar a shekarun 2006 a kan Fatah, ɓangarorin biyu sun ci gaba da zama a ware duk kuwa da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a Masar tsakanin sassan biyu a shekarun 2011. Wani kakakin ƙungiyar Fatah ya ce babu wani abu sabo da kuma ƙarin haske da ke cikin sanarwar ta Hamas wacce ke yin adawa da shirin tattaunawa da Isra'ila.

Masu aiko da rahotanni dai sun ce yankin na Gaza wanda Hamas ke riƙe da shi wanda ke kan iyaka da Masar ya samu komabaya tun bayan faɗuwar gwamnatin 'Yan Uwa Musulmi ta Mohammed Morsi.

Mawallafi: Abdourahmane Hassane
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe