1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar kisan jami'an Red Cross da 'yar Dapchi

October 15, 2018

Kungiyar Red Cross da al'ummar Dapchi sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta ceto Leah Sharibu da ma'aikatan agajin da Boko Haram ta kama domin kauce wa kisansu bayan cikar wa'adin da kungiyar ta ba da.

https://p.dw.com/p/36Xsx
Afrika - humanitäre Hilfe im Tschadsee-Gebiet
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

An shiga rudani da fargaba a garin Dapchi ganin cewa daga kowane lokaci mayakan Boko Haram na iya hallaka ma’aikatan jinya da ke aiki da kungiyar agaji ta Red Cross wanda suke garkuwa da su bayan cikar wa’adin da suka bayar na in ba a biya musu bukata ba za su hallaka su ya cika. Wannan ne ya sa hankalin iyayen Leah Sharibu da kawayenta da ma kuma sauran al’ummar garin Dapchi bayyana damuwa tare da yin roko ga gwamnatin Najeriya da kuma mayakan kungiyar da su yi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin an ceto Leah da Hauwa Mohammed da Alice Loksha da ma sauran wadanda kungiyar ke garkuwa da su.

Boko Haram lässt entführte Mädchen frei
Wasu daga cikin wadanda suka kubuta daga Boko Haram a garin DapchiHoto: Reuters/O. Lanre

Wata guda kenan da kungiyar Boko Haram ta hallaka Saifura Hussaini daya daga cikin ma’aikaciyar jinya da kungiyar ta kame a watan Maris tare da yin barazanar hallaka sauran ma’aikatan jinya da ma Leah Sharibu da suke garkuwa da su. 

Malama Rebecca Sharibu ita ce mahaifiyar Leah ba ta iya boye halin da take ciki a wannan lokaci ba yayin da take roko ga gwamnatin Najeriya. Malam Kachalla Bukar sakataren kungiyar iyayen da aka sace musu ‘ya‘ya a makarantar sakandaren Dapchi yana cikin masu wannan fata na ganin an sako yarinyar.

Nigeria - Massenentführung Boko Haram
Fargabar kisan jami'an Red CrossHoto: Getty Images/AFP/A. Abubakar

Tun a Lahadi ne dai kungiyar agaji ta ICRC ta roki gwamnatin Najeriya da kungiyar ta Boko Haram da su yi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin an ceto Hauwa Mohammed da Alice Loksha domin komawa ga iyalansu kamar yadda Mamadu Sow jami’in hukumar ya bayyana a kafar sadarwar zamani ta kungiyar.