Kira domin kawo karshen ayyukan kungiyar IS a Libiya | Labarai | DW | 17.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kira domin kawo karshen ayyukan kungiyar IS a Libiya

Kasashen Amirka da Faransa da Jamus da Italiya da Spain da kuma Birtaniya sun yi tir da ayyukan rashin imani da IS ke yi a Libiya.

Yaki da IS a birnin Sirte

Yaki da IS a birnin Sirte

Kasashen dai sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa ne tare da yin tir da kisan gilla da kuma ayyukan ta'addanci da rashin imani da kungiyar IS ke yi a Libiyan. Kungiyar ta IS dai ta kwace iko da birnin Sirte na Libiyan cikin watan Yunin da ya gabata tare da yanke kawunan mayakan sa kai 12 da suka yaki kungiyar lokacin da ta shiga yanki suka kuma bankare su a kan hanyoyin yankin kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar LANA ya ruwaito. Sanarwar da ke dauke da sa hannun gwamnatocin kasashen na Amirka da Faransa da Jamus da Italiya da Spain da kuma Birtaniya wadda ma'aikatar cikin gidan Amirka ta fitar a yammacin Lahadi, ta kuma bukaci dukkan bangarorin kasar ta Libiya da su hada karfi waje guda domin yakar barazanar da kungiyar IS din ke yi wa kasar baki daya.