1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kira da ɗaukar matakan gaggawa na ceto Siriya

June 7, 2012

Manzon ƙasashen duniya na musamman a Siriya Kofi Annan ya ce Siriya ta kai matsayin shiga yaƙin basasa babu ƙaƙƙautawa.

https://p.dw.com/p/15AJs
Hoto: Reuters

Wakilin ƙasashen duniya a Siriya kuma tsohon babban sakataren Majalisar ɗinkin Duniya Kofi Annan ya yi kira ga gamaiyar ƙasa da ƙasa da ta ɗauki matakan gaggawa a kan Siriya domin ƙasar ta kai wani matsayi na shiga yaƙin basasa gadan gadan. Mista Annan ya yi wannan kira ne a gaban babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya a wannan Alhamis.

A lokacin da yake jawabi a gaban wakilan ƙasashe 193 da suka hallara a zauren babbar mashawartar Majalisar Ɗinkin Duniya dake birnin New York manzon musamman na ƙasa da ƙasa a Siriya, Kofi Annan ya nuna takaicinsa ga sabon kisan ƙare dangi da aka yi a Siriya sannan ya yi kira da a ja kunnen shugaba Bashar Al-Assad game da taɓarɓarewar rikicin. Annan ya faɗa wa zauren taron na Majalisar ta Ɗinkin Duniya cewa rikicin Siriya ya ƙara yin muni, saboda haka idan ba a samu wani sauyi cikin gaggawa ba makomar ƙasar za ta zama ta mummunar tursasawa, kisan ƙare dangi, rikicin ƙabilanci da ma yaƙin basasa.

Rigingimu sun rincaɓe a Siriya

"Rikicin ya taɓarɓare, tashe tashen hankulan sun yi muni. Ana ci-gaba da cin zarafin mutane. Ƙasar na ƙara shiga mummunan yanayi na rigingimu. Maƙotan Siriya na sun damu matuƙa game da barazanar yaɗuwar rikicin."

Rahotannin kisan ƙare dangi da ya auku a ƙauyen al-Qubeir a ranar Laraba su suka mamaye zaman taron. Hotunan bidiyo sun nuna gawarwakin mata da yara yashe a gidajen gona dake ƙaramin ƙauyen na 'yan Sunni dake tsakiyar Siriya.

Syrien Massaker in Huola
Hoto: Reuters

"A nan ina nuna takaici na tare da yin tir dangane da sabon kisan ƙare dangi da ya auku a al-Qubeir na yammacin Hama inda aka kashe fararen hula ciki har da mata da ƙananan yara."

A kuma can ƙasar ta Siriya an yi harbi da ƙananan bindigogi a kan tawagar sa ido ta Majalisar Ɗinkin Duniya, dake ƙoƙarin shiga ƙauyukan da aka yi sabon kisan gillan da ake zargin sojoji magoya bayan shugaba Assad da aikatawa.

'Yan adawar Siriya da ƙasashen yamma da na yankin Gulf dake son ganin bayan Assad na ƙara saka ayar tambaya game da shirin Kofi Annan na wanzar da zaman lafiya da cewa ya ruguje saboda amfani da sojoji da gwamnatin Siriya ke yi don murƙushe boren da ake mata.

Babu zaman lafiya a Siriya sai Assad ya tafi

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta faɗa a birnin Santanbul na ƙasar Turkiya cewa zaman lafiya ba zai dawo Siriya ba matuƙar Assad na kan mulki.

Hillary Clinton in der Türkei
Hoto: AP

"Gwamnati ta tallafa wa aika-aikar da muka shaida ranar Laraba a Hama. Wannan rashin imani ne. Assad ya ninka matakan dabbanci da yaudara da yake ɗauka. Saboda haka Siriya ba za ta ga kwanciyar da zaman lafiya ko wani mulkin demokraɗiyya ba har sai Assad ya bar mulki."

Sai dai ƙawayen Assad kamar Rasha da China sun nuna goya baya ga wani sabon shirin Annan na kafa wata ƙungiyar tuntuɓar juna da za ta ƙunshi ƙasashen Rasha, China, Amirka, Birtaniya, Faransa da kuma manyan ƙasashen yankin dake da angizo kan gwamnatin Siriya da 'yan adawa wato kamar Saudiyya, Qatar, Turkiya da kuma Iran. Sai dai ƙasashen yamma na adawa da wannan sabon yunƙurin.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman