1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kimanin mutane 3000 sun rasa aiki a Ghana

Usman Shehu UsmanMay 17, 2015

Daruruwan 'yan kasar suka shiga zanga-zangar yin Allah wadai da yawaitar dauke wutar lantarki inda yanzu ayyukan kamfanoni da yawa suka tsaya cik abinda ke bazarana ga tattalin arzikin kasar

https://p.dw.com/p/1FR6n
Ghana - Arbeiter in der Schuhfabrik von Tonyi Senyaya
Hoto: DW/I. Kaledzi

Masu zanga-zangar da suka yi tattaki a babban birnin kasar Accra, sun bayyana cewa dole hukumomi su kawo karshenn matsalar da ake fiskanta da ta shafi karancin wutar lantarki. Daruruwan mutanen da dai sun bayyana takaicinsu, kan cewa duk da keraye-kirayen da jama'a ke yi, kan gwamnati ta dau mataki, amma kawo yanzu shugaba John Mahama kamar ya toshe kunnensa ne. Yanzu haka dai kimanin muta ne 3000 suka rasa ayyukansu bayan da kamfanoni suka rage ayyukansu bisa karancin makashi, abinda ya tilasta musu sallamar ma'aikata.