Kila-wa-kala a Burundi bayan juyin mulki | Labarai | DW | 13.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kila-wa-kala a Burundi bayan juyin mulki

Ba san wanda ke rike da iko ba tsakanin sojojin da suka yi ikirarin hambarar da shugaban Burundi da kuma shi Nkurunziza da jirginsa ya karkata akala zuwa Yuganda.

Sojojin da suka yi ikirarin hambarar da Pierre Nkurunziza daga karagar mulkin Burundi sun bada izinin rufe kan iyakokin kasar domin hana shugaban dawowa gida. Rahotannin da ke shiga mana da dumi-duminsu sun nunar da cewa an karkata akalar jirgin Pierre Nkurunziza zuwa wata kasa ta daban bayan da ya yi niyar sauka a filin tashi da saukan jiragen sama na Bujumbura. Da ma dai shugaba ya halarci taron koli da shugabannin yankin gabashin Afirka suka shirya kan rikicin kasar ta Burundi.

Da farko dai Fadar shugaban kasar Burundi ta nunar da cewa ta yi nasarar murkushe yunkuri juyin mulki da wasu wadanda ta danganta da fandararrun sojoji suka yi. Sannan ta na farautar wadanda suka yi yunkurin juyin mulkin.

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa dangane da halin da ake ciki a Burundi bayan da janar Godefroid Niyombare ya yi ikirarin hambarar da gwamnatin Pierre Nkurunziza. Cikin wata sanarwa da ya fitar da birnin New-York babban magatakardan Majalisar Ban Ki-moon ya yi kira da akai hankali nesa dangane da abin da zai iya biyo baya musaman ma a fannin tashin hankali.