1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Khalid Cheik Mohamed babban Pirsinan Gwantanamo

Yahouza S. MadobiMarch 15, 2007

Khalid Cheik Mohamed ya ɗauki alhakin kai harin 11 da watan satumber na 2001

https://p.dw.com/p/Btw0
Hoto: AP

Opishin Ministan tsaron Amurika, wato Pentagon, ya gabatar da jawabin da ya ce, Khalid Cheick Mohamed, mutumen nan da ake zargi da hannu dumu-dumu a hare-haren 11 ga watan satumber na shekara ta 2001 a Amurika, yayi, a yayin da aka yi masa tambayoyi, a gidan gwale-gwalen Gwantanomo da ke ƙasar Kuba,inda ake tsare da shi.

Khalid Cheik Muhamed, ta bakin wani sojan Amurika da ke wakiltar sa, ya ce daga farko har ƙarshe, shi ke da alhakin kitsa hare-haren ƙasar Amurika, wanda su ka hadasa mutuwar kussan mutane dubu 3,da kuma wasu sauran hare-hare, a sassa daban-daban na dunia da ƙungiyar Al´aida ta kai.

A cewar kakakin Mohamed Khalid, shi ne ke riƙe da matsayin babban darakta, mai kulla da tsarin kai hari na Usama Bin Laden, shugaban ƙungiyar Alka´ida.

A jimilce sanarwar ta Pentagone ta ce, Khaled Mohamed dan kasar pakistan, ya bayyana ɗaukar alhakin kai hare-haren a ƙalla 28 da sunan ƙungiyar al´ƙaida.

Wannan hare-haren sun jadda da na shekara ta 1993 a wanda ya rustsa da cibiyar hada-hadar kasuwancin ta Amurika wanda kumayayi sanadiyar mutuwar mutane 6.

Sai kuma harin birnin Bali na ƙasar Indonesia a shekara ta 2002,wanda ya jawo assara rayuka fiye da 200.

Kazalia da harin bama-baman da a ka kai, ƙasar Kenya a shekara ta 2002, wanda shima ya hadasa mutuwar mutane 14.

Khalid Mohamed inji sanarwar Pentagone, ya tabbattar da cewa, da shi ka ka kitsa harin ta´adancin da bai yi nasara ba, akan mirganyi Paparoma Jean Paule II da kuma shugaban ƙasar Pakistan Pervez Musharaf.

Yunƙurin harin baya-bayan nan da ya ke da hannu a cikin shine, wanda jami´an tsaro su ka bankaɗo a filin saukar jiragen samar Heathrow a ƙasar Britania.

A lokacin da na iya masa tambayoyin Khalid Mohamed ya ce ya fuskanci azaba a gidan kurkukun Gwantanamo .

A game da kuwa da harin na Amurika, ya nunar da cewa bai ji daɗi ba, da mutane kussan dubu 3 su ka rasa tayuka.

Sannan sanarwar da opishin ministan tsaroin Amurika ta bayyana ta ce Khalid ya ce ya yi wanan jawabi da raɗin kann sa ba tare da an yi masa wata tursasawa ba.

Idan dai ba a manta ba, a watan maris ne, na shekara ta 2003 jami´an leƙen asiri su ka capke Khalid Muhamed su ka kuma damƙa shi ga hukumomin Amurika.