1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kewaye gidan madugun adawa a Guinea

Yusuf Bala Nayaya
October 30, 2018

Akalla magoya bayan madugun adawar biyar ne suka samu raunika a taho mu gama da 'yan sandan da suka kewaye gidan madugun adawar dauke da kayansu na fada.

https://p.dw.com/p/37P4t
Guinea Präsident Wahlen Kandidat Cellou Dalein Diallo
Hoto: AP

Jami'an 'yan sanda a kasar Guinea sun yi kawanya a gidan madugun adawa na kasar Cellou Dalein Diallo, a wannan rana ta Talata domin hana shi shiga zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati a birnin Conakry da ke zama babban birnin kasar.

Akalla magoya bayan madugun adawar biyar ne suka samu raunika a taho mu gama da 'yan sandan da suka kewaye gidan madugun adawar dauke da kayansu na fada kamar yadda wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya bayyana.

Dan adawar da Shugaba Alpha Conde da ke kan karagar mulki tun a shekarar 2010 ya yi kira na a fita zanga-zangar a wannan Talata mako guda bayan da gwamnati ta haramta gangamin da Diallo ya ce 'yan sanda a kasar sun yi kokari na sace shi, zargin da 'yan sanda suka ki amincewa da shi. Dan adawar dai ya ce abin da 'yan sanda suka yi ya saba wa doka da 'yancin dan Adam.