1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kerry: Za mu iya katse hulda da Rasha

September 29, 2016

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya yi barazanar yanke tattaunawa da kasar Rasha idan ta ci gaba da yin baki biyu a kan rikicin Syriya musamman ma a birnin Aleppo.

https://p.dw.com/p/2QkS7
Sergei Lawrow John Kerry New York City
Hoto: picture-alliance/dpa/A.Shcherbak

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya gargadi kasar Rasha da cewar Amirka na kan bakarta ta yanke duk wata hulda da ita a tattaunawar da suke yi game da kasar Siriya, matukar ita Rashar bata taka rawar gani wajen kawo karshen luguden wuta da ake yi a birnin Aleppo ba.

An dauki lokaci mai tsawo kasashen Amirka da Rasha suna zargin juna kan rikicin na Siriya da ya ki ci ya ki cinyewa, to amma Amirka na ganin lokaci ya yi da za ta soke duk wata tattaunawa da takwarartata wato Rasha har sai an tsawatarwa dakarun da ke yin biyayya ga gwamnati Bashar al-Assad don tsagaita wuta a gabashin birnin Aleppo inda 'yan tawaye ke iko da shi.


To sai dai Moscow ta ce wannan tauna tsakuwa da Amirkan ke yi ba zai yi tasiri ba, kuma ta yi Allah wadai da irin wannan ikirari da Amikan ta yi. Majalisar Dinkin Duniya dai ta kirayi dukkanin kasashen biyu da su daina siyasa da rayukan fararen hula.