1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kerry ya nemi sulhu tsakanin 'yantakara a Kabul

August 7, 2014

Sakatare Kerry na harkokin wajen Amirka ya nemi 'yan takarar shugaban kasa a Afghanistan su daidaita tsakaninsu dan kaucewa yakin basasa.

https://p.dw.com/p/1Cr6G
US-Außenminister John Kerry in Afghanistan mit Ashraf Ghani und Abdullah Abdullah
Hoto: Reuters

Sakataren kula da harkokin wajen Amirka John Kerry ya isa birnin Kabul a wannan Alhamis din domin ya shiga tsakanin 'yan takarar mukamin shugabancin kasar, wadanda suka fara gaba da juna, a dalilin sakamakon zaben da aka fitar wanda ke barazana ga shirin samar da zaman lafiya a kasar bisa la'akari da janyewar dakarun kungiyar kawancen tsaro ta NATO.

Akwai zarge-zargen cewa an tabka magudi a zaben shugaban kasar da aka yi a watan Yuni, abin da ya jefa kasar cikin rikicin siyasa, kuma ya sanya Majalisar Dinkin Duniya, bayyana fargabar cewa mai yiwuwa halin da kasar ta shiga ya mayar da ita cikin wani yanayi na yakin basasa, kamar yadda ya kasance a shekarun 1990.

Ko a watan da ya gabata, Kerry ya ziyarci Kabul domin yin yarjejeniya da abokan hammayar, inda Ashraf Ghani da Abdullah Abdullah suka amince a sake kidaya kuri'un wadanda suka kai kusan milliyan takwas, su kuma girka gwamnatin hadin gambiza.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Mohammadu Nasiru Awal