Kerry ya ce duniya za ta gama karfi don yakar IS | Labarai | DW | 10.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kerry ya ce duniya za ta gama karfi don yakar IS

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya ce kasar Amirka da duniya baki daya za su yi wa mayakan kungiyar IS mai fafatukar kafa kasar Islama taron dangi.

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya ce kasar Amirka da sauran kasashen duniya ba za su tsaya su zura ido suna kallon sojojin sa kai na kungiyar IS suna aikata ta'asa da yi wa mutane kisan gilla ba. Kerry ya fada wa wani taron manema labarai a Bagadaza babban birnin Iraki cewa yaki ne da al'ummar Iraki za ta yi nasara, amma kuma ya zama wajibi sauran kasashen duniya su hada karfi don yakar wannan kungiya.

"Ta'asar da suke aikatawa da hali na dabbacin da suke nunawa basu da gurbi a wannan duniya. Yaki ne da ya zama wajibi al'ummar Iraki ta yi nasara. Yaki ne da ya zama dole kasar Amirka da kuma sauran kasashen duniya su taimaka ga kowane matakin da za a dauka."

Kerry dai ya je birnin Bagadaza ne inda ya gana da sabbin mahukuntan Iraki, sannan ya yi musu alkawari Amirka za ta ba su goyon baya don fatattakar kungiyar IS da kuma barazanar da take haddasawa.

A ci gaba da tashe tashen hankula a Irakin mutane 17 sun rasu sannan 58 sun samu raunuka a wani harin bam da aka kai da mota a birnin Bagadaza yayin wannan ziyara ta Mr. Kerry.