1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenyatta zai halarci zaman kotun ICC

October 6, 2014

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ce zai halarci zaman kotun kasa da kasa da ke hukunta masu aikata manyan laifuka, domin amsa tambayoyi a tuhumar da kotun ke masa.

https://p.dw.com/p/1DRGZ
Hoto: Simon Maina/AFP/Getty Images

Kotun ta ICC dai na tuhumar na Kenyatta da hannu a rikicin bayan zabe na shekara ta 2007 da aka yi a Kenya, wanda kuma ya haddasa asarar rayuka masu yawa. Kenyatta ya shaidawa 'yan majalisar dokokin kasar cewa zai wakilta mataimakinsa William Ruto a matsayin mukaddashinsa a yayin da zai halarci zaman kotun a helkwatarta da ke birnin The Hague na kasar Netherlands cikin wannan mako. Shi ma dai mataimakin nasa William Ruto na fuskantar irin wannan tuhuma daga kotun ta ICC. Wannan dai shine karo na farko da wani shugaba da ke kan karagar mulki zai gurfana a gaban kotun ta ICC, da ke shan suka daga kasashen Afirka masu yawa bisa zargin nuna son kai da suke yi wa kotun, suna masu cewa shugabannin Afirka kawai take sanyawa idanu.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo