Kenya za ta rufe makarantun tsangaya | Labarai | DW | 24.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kenya za ta rufe makarantun tsangaya

Mahukunta ƙasar sun ce za su rufe makarantun tsangaya na islamiya waɗanda ta ce ake girkawa da nufin yaɗa haƙidar masu da'awar ta'addanci.

Tuni da gwamnatin ta rufe wata makarantar allon a garin Machakos wanda ke da ratan kilomita 60 daga kudu maso gabashin birnin Nairobi babban birnin ƙasar.Bayan da aka kame daliban makarantar su kusan 30 waɗanda ake zargin cewar Ƙungiyar al Shaabab ta Somaliya na ɗaukarsu domin yin jahadi.

Shugaban hukumar 'yan sanda na ƙasar ta Kenya ya ce bayan wannan makarantar sun saka ido a kan sauran makarantu na allo a garuruwan Monbasa da sauran yankunan ƙasar.