Kenya: ′Yan sanda sun kashe masu zanga-zanga | Labarai | DW | 13.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kenya: 'Yan sanda sun kashe masu zanga-zanga

Rahotanni daga Nairobi babban birnin kasar Kenya na cewa rayuka sun salwanta a wata arangamar tsakanin masu bore da jami'an 'yan sanda a yammacin kasar.

Daruruwan masu goyon bayan bangaren adawar kasar ne dai suka bijirewa dokar da ta haramta zanga-zanga, wadda gwamnatin Kenya ta ayyana sakamakon zaben shugaban kasa da ake tababa a kansa. A mahaifar madugun adawa Raila Odinga wato Bondo, wani gungun masu boren sun sha harbe-harbe daga jami'an 'yan sanda, lokacin da suka far wa wani caja ofis da ke garin.

Can kuma a yankin Kisumu mai tazarar kilomita 50 daga garin na Bondo, shaidu sun ce wasu mutane 20 na can kwance a asibiti, hudu daga cikinsu dauke da raunin bindiga. Tuni dai ofishin tsaro da ke shiyar ya tabbatar da mutuwar mutane biyu a arangamar.