Kenya: ′Yan fafutika sun nemi a dage zabe | Labarai | DW | 24.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kenya: 'Yan fafutika sun nemi a dage zabe

Kotun kolin kasar Kenya ta kira wani zama na gagawa domin tattauna batun wani kara da wasu masu fafutikar kare hakin bil-Adama suka shigar a gabanta na ta dage zaben.

Kenia Oberstes Gericht annuliert Wahlen (picture-alliance/AP Photo/B. curtis)

Kotun kolin kasar Kenya

Masu shigar da karan sun ce dalilinsu na yin hakan shi ne na ganin cewa Kenya da hukumar zabenta ta IEBC ba su shirya gudanar da zaben na ranar Alhamis ba, wanda hukumar zaben ta kira bayan soke zaben na farko da kotun tsarin mulkin kasar ta yi bayan hukumar zaben ta ayyana shugaban kasar mai ci Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben.

A wannan Talata ne dai shugaban kotun kolin kasar ta Kenya David Maraga, ya sanar da wannan mataki na kiran zaman kotun a gobe Laraba da misalin karfe 10 a gogon kasar karfe bakwai agogon GMT, inda ya umarci hukumar zaben kasar da ma 'yan takarar da su gabatar da na su korafi idan har suna da shi kafin karfe 08.30 na safiyar Laraba. Masu shigar da karan dai sun ce janyewar dan takara Raila Odinga daga zaben, da ma korafin da shugaban hukumar zaben ya yi na yuyuwar kasa gudanar da safifin zabe, na daga cikin dalillansu na neman a daga zaben na Kenya.