Kenya: Takaddama a kan samakon zabe | Labarai | DW | 11.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kenya: Takaddama a kan samakon zabe

'Yan adawa a Kenya sun ce ba, za su halarci taron hukumar zaben kasar ba, na bayyana sakamakon zaben da suka ce an yi magudi.

Wani jigo daga hadin gwiwar 'yan adawar James Orengo ya ce shigar da kara a gaban kotu ba hanya ce ba da suke ganin ta kwato hakkinsu. Sannan kuma kungiyar ta gargadi hukumar zaben da ta dau lokaci mai tsawo kuma ka da ta yi gaggawa wajen bayyana sakamakon zaben domin tantance kura-kuran da aka samu. Kungiyar 'yan adawar ta yi zargin cewar an yi magudi a zaben da aka fafata tsakanin Raila Odinga da kuma Uhuru Kenyatta