Kenya ta cika shekaru 50 da samun yancin kai | Siyasa | DW | 12.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kenya ta cika shekaru 50 da samun yancin kai

Al'ummar Kenya na gudanar da shagulgulan samun 'yanci daga Birtaniya, dab da lokacin da ƙasar ke alfaharin zama mafi ƙarfin tattalin arziki a gabashin Afirka.

Kenya dai ƙasa ce da ke sahun farko wajen ƙarfin tattalin arziki a gabashin Afirka, inda ta ke samun bunƙasa na kaso 5 cikin 100 duk kuwa da matsalolin cin hanci da ke neman zama ruwan dare a ƙasar. Kazalika, ta samu nasarar ce duk da shari'ar da shugaban ƙasar Uhuru Kenyatta, da kuma mataimakinsa William ruto ke fuskanta a gaban kotun hukunta manyan laifukan yaƙi da ke birnin the Hague, baya ga ƙalubalen tsaron da ta ke fama da shi sakamakon rawar da ta ke takawa ta fannin yaƙi da masu tada zaune tsaye a ƙasar Somaliya da ke makwabtaka da ita. Fiye da kaso 60 na al'ummar Kenya dai, matasa ne 'yan ƙasa da shekaru 24 a duniya. sun kuma bayyana ra'ayoyinsu yayin da suke wani shagon yanar gizo da ke a Nairobi babban birnin kasar.

Ra'ayoyin 'yan ƙasar ta Kenya dangane da ranar samun yancin kai

Kenia Unabhängigkeitstag 12.12. 2013

Shugaba Uhuru Kenyatta

Sunana Sibylle Munyika. ''Mafi rinjayen al'umma na rayuwa ne hannu baka - hannu kwarya, domin kuwa ba su da wuraren kwana, kuma matasa ba su da ayyukan yi. Inda ma da a ce muna da shugabannin da ke gujewa cin hanci.'' Sai kuma wata ɗalibar sashen sadarwa mai suna Joane Ochieng Onyango. Ta ce : ''Ƙasar na samun ci gaba ta fannin fasaha, amma akwai ɗimbin ƙalubale, domin kuwa ƙasar ba ta samu bunƙasa sosai ba. Shi kuwa wannan ɗalibin mai suna Louis ɗan shekaru 19 a duniya ''Cewa yake abin farin ciki ne cika shekaru 50 da samun 'yanci.'' Kamata yayi mu yi alfahari da irin ci-gaban da muka samu, kuma muna jin dadi..Shi kuwa Samuel da ke aiki a wani kamfanin aike wa da saƙonni cewa yayi:''Mun fi jin dadi idan ka kwatantamu da mutanen da suka rayu a shekaru 50 da suka gabata, domin muna cin gajiyar fasaha da ci gaban zamani da kuma na yada labarai."

A tsawon shekaru 50 an samu bunƙasar ci gaban fasaha

Kenia 50 Jahre Unabhängigkeit

Taron bukin cika shekaru 50 na Kenya

Yayin da Kenya ta cika shekaru 50 da samun 'yanci dai tana cike da alfaharin samun bunƙasa a fanin fasaha, inda 'yan ƙasar ke yin amfani da wayar sadarwar tafi da gidanka wajen aike wa 'yan uwansu kuɗaɗe, kuma gano albarkatun ruwa da kuma na man fetur a yankin hamadar ƙasar a baya bayan nan, ka iya taimaka wa ci-gaban tattalin arzikinta. Wani batun da zai taimaka wa ci-gaban ƙasar Kenya kuwa a cewar Auma Obama, wadda ke zama 'yar uwa ga shugaban Amirka Barak obama, kana ta ke shugabantar gidauniyar Sauti Kuu a ƙasar, shi ne shawo kan rigingimun ƙabilanci a ƙasar ta Kenya, musamman irin waɗanda suka biyo bayan zaɓukan ƙasar a shekara .Ta ce " A ganina akwai buƙatar 'yan Kenya su ƙara mutunta junansu. Ina ganin muna da ɗabi'ar tsananta wa juna. bai dace mu rinƙa nuna ƙabilanci ba. Idan muna tuna batun ci gaban ƙasarmu, kamata yayi mu san cewar taimaka wa wasu, taimakon kai ne." Sai dai kuma wani ƙudirin dokar baya bayan nan da ya tanadi ƙarfi fiye da ƙimar da hukumomi ke da shi a kan irin abubuwan da kafofin yaɗa labarai ke bayyana wa jama'a na daga cikin abubuwan da wasu 'yan ƙasar, dama saura ƙasashen duniya ke nuna damuwa a kansa, bisa abin da 'yan jarida a ƙasar ke cewar ka iya durƙusar da aikinsu, kasancewar yana karan tsaye ne ga tsarin mulkin ƙasar.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi : Saleh Umar
Edita : Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin