Kenya ta amince da doka kan tsaron kasa | Labarai | DW | 19.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kenya ta amince da doka kan tsaron kasa

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya amince da sabuwar dokar nan kan batun tsaro wadda ta haifar da cece-kuce har ma da baiwa hamata iska a majalisar dokokin kasar

Cikin jawabin sa, Shugaba Kenyata ya nuna rashin jin dadinsa ga halayyar da 'yan majalisa na bangaran adawa suka nuna a majalisar yayin kada kuri'u kan wannan doka. Tun a jiya Alhamis kwamitin da ke kula da kiyaye bin dokoki da kuma yaki da cin hanci na (EACC) a kasar ta Kenya, ya ce zai soma wani bincike kan halayyar wasu 'yan majalisun dokokin kasar, wadanda kwamitin ke ganin sun taka ayar doka mai lamba shidda ta kundin tsarin mulkin kasar ta Kenya, da ke cewa bai kamata ba ma'aikaci ya zubar da mutuncin ma'aikatarsa. Burin wannan doka dai shi ne na kare rayuwar al'umma da kuma dukiyoyinsu a cewar shugaban kasar ta Kenya yayin da yake jawabi.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou awal Balarabe