Kenya: Dan sanda ya harbe matarsa da kansa | Labarai | DW | 07.12.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kenya: Dan sanda ya harbe matarsa da kansa

Wani jami'in dan sanda na kasar Kenya ya bindige mutane shida ciki har da matarsa daga bisani kuma ya juyo ya harbi kansa. Lamarin da ya faru a wannan Talata a birnin Nairobi na kasar Kenya ya haifar da zaman zullumi. 

Rundunar 'yan sandan kasar Kenya ba ta kai ga fitar da wata sanarwa kan lamarin ba. Sai dai rahotanni sun ce dan sandan ya fara harbe matarsa ne, inda daga baya kuma ya juya kan mutanen da suka zo wucewa su ma ya bude musu wuta. 

Kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA ya ce lamarin ya haifar da zanga-zanga daga wasu matasa da suka fara kona tayoyi suna kira da lallai sai an biya su diyyar mutanen da ake zargin dan sanda  ya halaka.