Kenya: Binciken rantsar da Raila Odinga | Labarai | DW | 31.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kenya: Binciken rantsar da Raila Odinga

Gwamnatin Kenya na binciken rantsar da kansa da madugun 'yan adawar Kenya ya yi, domin nazarin ko hakan ya cancanci daukar matakin hukunci a kansa.

A jiya Talata ne dai, Odinga ya rantsar da kansa a matsayin shugaban jama'a a birnin Nairobi a bainar dubban magoya bayansa, bisa ikirarin gwamnatin Uhuru Kenyatta haramtacciya ce.

Sanarwar gwamnati na bayyana matakin na jiya, a matsayin yunkurin kifar da zababbiyyar gwammatin Janhuriyar Kenya. Gabannin bukin rantsar da Odinga dai, babban Alkalin Kenyan ya yi gargadin cewar, wannan yunkuri tamkar cin amanar kasa ce.

Ya zuwa yau Laraba dai wasu gidajen talabijin masu zaman kansu na cigaba da zama a rufe, matakin da gwamnati ta ce na bangaren binciken da take gudanarwa dangane da yayata rantsar da madugun 'yan adawar.