Kazamin fada a kasar Kongo
April 2, 2013A wani rikicin da ya barke a 'yan kwanakin baya bayan nan a kasar ta Jamhuriyar Demokradiyar Kongo, rahotani sun tabbatar da kimanin mutane 23 ne dai suka kwanta damarsu tun bayan barkewar rikicin a makon nan da ya shige a yankin Lubumbashi inji kakakin gwamnatin kasar ta Kongo.
A kwanan baya ne dai aka yi wani artabu tsakanin dakarun gwamnatin da mayakan kungiyar Mai-Mai yayinda sama da mutane 54 suka samu raunuka ciki har da fararen hula kamar yadda sanarwar ta gwamnatin ta bayanar.
Rahotani sun ce mayakan sun kutso ne daga yankin katanga mai dimbin arzikin ma'adinai inda sukayi masayar wuta da dakarun gwamntai da suka samu goyon bayan sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.
Dama dai tun wajajan shekarun 1960 ne yankin na Katanga ya tada kayar baya na bukatar samun 'yancin gashin kansa a matsayin kasa mai cikakken iko.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Saleh Umar Saleh