Kawo ƙarshen Ebola cikin gaggawa | Labarai | DW | 01.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kawo ƙarshen Ebola cikin gaggawa

Shugaban shirin Majalisar Ɗinkin Duniya na yaƙi da cutar Ebola mai saurin kisa da ta adabi yankin yammacin Afirka Anthony Banbury, ya sha alwashin shawo kan cutar nan da ɗan lokaci.

Banbury ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a shelkwatar majalisar da ke birnin New York na Amirka inda ya ƙara da cewar zai yi aiki tukuru domin kawo ƙarshen cutar.

"Majalisar Ɗinkin Duniya tana aiki cikin gaggawa domin kawo ƙarshen wannan cutar, a yanzu haka mun mayar da hankali wajen yin aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki da suka hadar da jami'an kiwon lafiya da ma sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke yankunan da suke fama da Ebola domin ganin mun kaawo ƙarshen cutar kafin ta fi ƙarfinmu".