Kawancen Merkel ta CDU da Seehofer na CSU na sake rauni | Labarai | DW | 30.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kawancen Merkel ta CDU da Seehofer na CSU na sake rauni

Duk da tsawon lokaci da aka dauka ana tare a shekarar bara Seehofer ya zame wa Shugabar gwamnati Merkel sartsen kafa bayan da ya yi ta maimaita cewa sai ta taka birki ga shirinta na tarbar baki.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ba za ta halarci taron jam'iyyar kawancenta ba a jihar Bavaria kamar yadda wata majiyar kawar jam'iyyar ta bayyana a ranar Asabar din nan, abin da ke zuwa bayan watanni na cece ku ce kan tsarin shugabar na 'yan gudun hijira.

Merkel wacce ke jan ragama ta jam'iyyar CDU da Horst Seehofer jagoran jam'iyyar CSU sun amince a ranar Juma'a cewa ba za ta halarci taron na Munich ba, wani abu da ya nuna ta ware daga tsohon tsari a gwamman shekaru. Duk da tsawon lokaci da aka dauka ana tare a shekarar bara Seehofer ya zame wa Shugabar gwamnati Merkel sartsen kafa bayan da ya yi ta maimaita cewa sai ta taka birki ga shirinta na tarbar baki a Jamus, kiran da ta toshe kunnenta har sai da bakin haure 800,000 su ka shiga kasar a 2015.