Kawance tsakanin EU da Turkiyya | Labarai | DW | 06.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kawance tsakanin EU da Turkiyya

Kungiyar tarayyar Turai ta EU gami da mahukuntan Turkiyya sun kawo karshen rashin jituwar da ke tsakaninsu shekara da shekaru.

Bayan da wasu manyan jiga-jigan kungiyar tarayyar Turai ta EU suka ziyarci shugaba Racep Tayyip Erdogan a fadarsa da ke Ankara a yau din nan.

Shugabar hukumar ta EU Ursula von der Leyen da abokin aikinta na majalisar kungiyar Charles Michel sun tattauna kan batun sake dawo wa da kyakyawar alaka tsakanin Turkiyya da kasashe mambobin kungiyar  EU, inda suka sha alwashin bude sabon babin dangantaka a tsakaninsu.

Dangantakar dai ta yi tsami ne sakamakon ja in jar da ta shiga tsakanin Turkiyyar da kasashen Cyprus da Girka kan batun mallakar ruwan da ya ratsa kasashen.