Kauracewar zaman lafiya a Iraqi | Labarai | DW | 15.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kauracewar zaman lafiya a Iraqi

Ga dukkan alamu kasar Iraqi na neman zamowa wata cibiyar tashe-tahsen hankula da zub da jini, inda a kowace rana ake kashewa tare da jikkata mutane da dama.

Wasu jerin hare-hare a Iraqi da suka hadar da bama-bamai da aka dasa a motoci, sun yi sanadiyar mutuwar mutane 28 a ranar Lahadi, yayin da shugaban wata gunduma a Bagadaza babban birnin kasar ya tsallake rijiya da baya a yunkurin kashe shi da aka yi.

Wanna dai shine tashin hankali na baya-bayan nan bayan kwashe tsahon watanni da aka yi ana zub da jini, a wani abu da aka bayyana da mafi muni tun daga shekara ta 2008, wanda hakan ke nuna fargabar cewa Iraqi za ta koma cikin rikicin ban-bancin akida da ya haddasa mutuwar dubban mutane a shekarun baya.

Tuni dai aka sanya dokar takaita zirga-zirga a Bagadaza da wasu sassan kasar, tare kuma da kaddamar da farautar masu tada kayar baya, sai dai kuma hakan bai hana kai jerin hare-hare a sassa da dama na kasar ba.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu