1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi mai sana'ar hotuna a Katsina

January 23, 2019

Wani matashi a Katsina da ya kammala karatun HND bangaren aikin jarida babu aikin yi, ya bude gurin kwamfuta inda yake sana'ar tace hotuna masu motsi watau bidiyo dama daukar hotunan wurin tarukan daurin aure ko suna.

https://p.dw.com/p/3C1AY
Wannan wani tsohon hoto ne mu ka yi amfani da shi na wani taron masu daukar hotuna da aka yi a Lagos
Wannan wani tsohon hoto ne mu ka yi amfani da shi na wani taron masu daukar hotuna da aka yi a LagosHoto: DW/A. Kriesch

Wannan matashi Ibrahim Rafuka ya kammala karatunsa ne tun shekara 2013 ya nemi aiki kuma bai samu ba, shi  ya sa ya yanke shawarar nema wa kansa mafita kuma a cewarsa ya ga amfanin hakan: "Bayan na kammala karatuna, na Diploma kuma na yi HND kasancewar ban samu aiki ba sai na yi tunanin cewar yana da kyau  na yi wata sana'a don samun aiki ba tare da na yi dogaro da wani ba. Wannan shi ya bani damar na koyi sana'ar daukar hoto na bidiyo, na samu nasarori sosai saboda na yi aure kuma ina dogaro da kai ina taimakon wasu musamman kannena wajen sha'anin karatunsu. " Sai dai matashin dukka kalubalen da yake kuskanta bai hanasa cigaba da sana'ar ba ganin duk lokacin da ya fita yakan samun abin da zai korewa bakinsa kuda dama iyalinsa.