Katsina: Matasa sun fusata kan rashin tsaro | BATUTUWA | DW | 16.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Katsina: Matasa sun fusata kan rashin tsaro

Matsalar rashin tsaro da ke kara ta'azzara a Najeriya ta fusata matasan jihar Katsina, inda suka gudanar da wata zanga-zangar lumana da nufin tilasta mahukunta su dauki mataki.

Nigeria Katsina Sicherheit

Zanga-zangar lumana kan rashin tsaro a jihar Katsina da ke Najeriya

Matasan dai sun yi jerin gwano a Katsinan ne karkashin jagorancin hadakar kungiyoyin matasa a jihar, inda suka dauki haramin zanga-zangar tasu daga fadar mai martaba sarkin Katsina suka kuma kitse ta a fadar gwamnati. Koda yake wasu bata gari sun so kawo nakasu ga masu zanga-zangar da ta kasance ta lumana, sai dai Hamza Yunusa Jibiya da ke zaman guda daga cikin matasan da suka shirya wannan jerin gwano, ya bayyana cewa jami'an 'yan sanda sun kawo musu dauki.

Da yake jawabi ga masu zanga-zangar yayin da ya karbe su, kwamishinan 'yan sandan jihar ta Katsina Sanusi Buba ya kwantarwa da matasan hankulansu, yana me bayyana musu cewa mahukunta na sane kuma suna kokarin shawo kan matsalar.

Nigeria Katsina Sicherheit

Matasa sun gaji da kisan da ake a Katsina

Matasan dai sun fusata ne sakamakon yawaitar hare-haren 'yan bindiga a jihar dama makwabtanta, wandanda ke kai farmaki su kashe mutane da yi wa mata fyade kana su yi awon gaba da dabbobi da dukiyoyin jama'a.

Masu fashin baki kan al'amuran tsaro dai, na ganin tilas sai gwamnati ta dauki matakan da suka dace domin shawo kan matsalar, in har ba a son wannan zanga-zanga ta fantsama zuwa sauran jihohin arewacin kasar da su ma ke fama da matsalar tsaron. Jihar Katsina dai na zaman mahaifa ga shugaban kasar mai ci yanzu Muhammadu Buhari kuma ta jima tana fuskantar matsalar rashin tsaro.

Rahotanni sun nunar da cewa a yanzu haka akwai dinbin 'yan gudun hjira, mafi akasarinsu mata da kananan yara da ke watse a makarantun firamare, cikin halin dimuwa da rashin abinci da ma sauran kayan masarufi.

 

 

Sauti da bidiyo akan labarin