1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamfanin Facebook ya roki gafarar duniya

Mohammad Nasiru Awal
October 5, 2021

Bayan matsalar katsewar sadarwa da kamfanin Facebook ya fuskanta tsawon awanni shida, shugaban kamfanin Mark Zuckerberg ya ba wa ma'abota shafukan sada zumunta hakuri bayan da komai ya daidaita.

https://p.dw.com/p/41IY2
Störung | WhatsApp, Facebook und Instagram
Hoto: Ozge Elif Kizil/AA/picture alliance

Tsawon awanni shida aka kwashe abubuwa sun tsaya cak a hanyoyin sadarwa a shafukan sada zumunta na Facebook wanda daga bisani kamfanin ya tabbatar da samun matsala a hanyoyin sadarwarsa na Facebook da Instagram gami da WhatsApp. Lamarin ya zo lokacin da kamfanin na Facebook ke tsakiyar rikicin fallasa kan cewa suna binciken irin illar da yawan zama a kan shafin da mutane musamman matasa suke yi ke shafar rayuwarsu.

Kamfanin ya ce matsalar ta auku ne sakamakon aikin inganta wani bangarensa, wanda ya kai ga garin gyaran gira aka rasa ido. Sama da mutum biliyan uku ne suka kasa shiga shafukansu, wanda hakan ya janyo asara mai yawa ga kamfanoni. Shi ma kamfanin na Facebook ya tafka babbar asara ta dimbin miliyoyin dalar Amirka a cewar masana.

Mark Zuckerberg a babban taron duniya kan sha'anin tsaro a Munich, Jamus a shekarar 2020
Mark Zuckerberg a babban taron duniya kan sha'anin tsaro a Munich, Jamus a shekarar 2020Hoto: picture-alliance/AA/A. Hosbas

Wannan matsalar dai na zuwa ne a daidai lokacin da wata tsohuwar ma'aikaciyar kamfanin ta fallasa yadda kamfanin ke ba da fifiko a kan kudaden da yake samu maimakon kan yadda mutane musamman ma matasa ke bata lokaci a shafukan sadarwar kamfanin.

Su ma kafafen yada labarai manya da kanana na amfani da shafukan na sada zumunta, kuma katsewar hanyoyin sada zumunta ta shafi ayyukansu musamman a huldarsu da masu bibiyarsu ta shafukan sada zumunta.

Mamallakin Facebook Marc Zuckerberg da ya bayyana aukuwar lamarin da mummunan abin bakin ciki ya roki gafarar ma'abota shafukan sada zumunta ya kuma ba su hakuri bayan da komai ya daidaita a shafukan na sada zumunta.