Katar: Erdogan ya gana da Sarki Salman | Labarai | DW | 23.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Katar: Erdogan ya gana da Sarki Salman

A wani mataki na neman warware rikicin diflomasiyyar ta ya kunno kai tsakanin Katar da makwabtanta, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana a wannan Lahadi da Sarki Salman na Saudiyya.

Saudi-Arabien Reccep Erdogan & König Salman bin Abdulaziz Al Saud (picture-alliance/Anadolu Agency/Turkish Presidency/Y. Bulbul)

Shugaba Erdogan na kasar Turkiyya tare da Sarki Salmane na Saudiyya a birnin Jeddah.

Wannan ziyara ta Shugaba Erdogan a birnin Jeddah na zaman mataki na farko na rangadin da zai kai a wasu kasashen yankin Gulf a wani mataki na neman sasanta rikicin diflomasiyyar da ya kunno kai tsakanin kasar Katar da sauran kasashe makwabtanta da suka hada da Saudiyya da Bahrain da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa wadanda suke zargin Katar din da goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda.

Duk da cewa ana yi ma sa kallon na kusa da kasar Katar, shugaban kasar ta Turkiyya ya gabatar wa kasashen gudunmmawa ta shiga tsakani don sasanta wannan rikici, inda a cewar kamfanin dillancin labarai na SPA sarkin na Saudiyya ya tattauna da Shugaba Erdogan kan matsalolin tattalin arzikin yankin da kuma kokarinsu na yaki da ta'addanci da ma hanyoyin da 'yan ta'addan ke samun kudadan shiga.

Da yammacin wannan rana ta Lahadi Shugaba Erdogan na Turkiyya zai fice daga Saudiyya zuwa kasar Kuwait sannan a ranar Litinin ya nufi kasar Katar. Tun dai a ranar biyar ga watan Yulin ya gabata kasashen na Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya suka sanar da yanke huldar diflomasiyya da kasar ta Katar tare da kakaba ma ta jerin takunkumi.