Kasuwar baje kolin kananan dabbobi saboda layya | Zamantakewa | DW | 23.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Kasuwar baje kolin kananan dabbobi saboda layya

Hukumomin Nijar da kungiyoyin ba da tallafi na duniya da ke aiki a kasar suka jagorancin kasuwar baje kolin dabbobin layya.

A karo na farko hukumomi a Jamhuriyar Nijar tare da tallafin masu hannu a shuni na kasa da kasa irin hukumar USAID ta kasar Amirka suka bude wata kasuwar baje koli da kananan dabbobi dangin tumaki da awaki a garin Maradi. Bude kasuwar ya zo daidai da lokacin da al'umar musulmin kasar ta Nijar suke shirye-shiryen bikin salla babba.

Masu saye da sayarwa dai sun cike kasuwar suna tafiyar da harkokin ciniki jim kadan bayan bikin bude kasuwar. Kasuwar dai ta samu halarta masu saye da sayarwa maza da mata daga ko-ina cikin kasa da ma makwabciyar kasa Najeriya.

Garba Mahaman daya daga cikin shugabannin da suka shirya kasuwar ya yi karin haske game da manufa da gurin shirya wannan kasuwar inda ya ce:

"Tana sa hulda tsakanin makiyaya da masaya. Kasuwar wata mahada ce da za ta sa su karfafa ayyukansu kuma su san juna tsakanin na Nijar da na kasashen makwabta. Lalle wannan ita ce kasuwa ta farko muna son mutane su gamsu da ita su kuma yaba, haka zai sa mu maimata shi kowace shekara."

Kasuwar ta yi nasara kuma jama'a ta yaba da tsari da matakan da aka dauka dan kasuwar ta gudana cikin kwanciyar hankali. To sai dai duk da haka farashin dabbobin bai gamsar da galibin masaya ba kamar yadda wasunsu suka bayana cewa sun yi mamaki yadda farashin bai sauki ba idan aka kwatanta da kasuwar dabbobi bisa al'ada.

Kasuwa ta ci cikin sa'a da nasara

Kasuwar ta samu halarta masaya baki daga tarrayar Najeriya. Alhaji Malam Murtala daga jihar Kano ya bayana ra'ayinshi game da wannan kasuwar baje koli ta kananan dabbobi yana mai cewa:

"Gaskiya na zo na ga wannan kasuwar baje kolin raguna, kuma a kasuwar ba irin dabbobin da babu. Farashinsu kuma ya banbanta. An bude dai kasuwar cikin sa'a da nasara. Zan saye da yawa in aika su Najeriya. Dukm wanda ya nema zai samu daidai karfinsa."

Baya ga masu saye da sayarwa an kuma samu 'yan kallo wadanda suka je domin kashe kwarkwatar idonsu.