1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasuwanci mara shinge a Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 22, 2018

Kasashen Afirka 44 sun rattaba hannu kan fara amfani da yarjejeniyar kasuwanci mara shinge a tsakaninsu cikin watanni 18 masu zuwa, da nufin bunkasa kasuwanci da tattalin arzikinsu.

https://p.dw.com/p/2uoKD
Shugabannin kasashen Afirka a taron kungiyar Tarayyar Afirka a Kigali
Shugabannin kasashen Afirka a taron kungiyar Tarayyar Afirka a Kigali Hoto: Getty Images/AFP/STR

Yarjejeniyar da ake wa lakabi da "African Continental Free Trade Area (CFTA)" a takaice, an sanya hannu a kanta ne yayin taron kungiyar Tarayyar Afirka a Kigali babban birnin kasar Rwanda. A jawabinsa, shugaban karba-karba na Tarayyar Afirkan kana shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame cewa ya yi abin da suka yi la'akari da shi wajen cimma wannan yarjejeniya shi ne mutuntaka da jin dadin 'yan Afirka da suka hadar da manoma da ma'aikata musamman mata da matasa. Ya kara da cewa:

"Dalilin daukar alkawarin kasuwanci mara shinge da kuma zirga-zirga ga al'ummar Afirka baki daya, shi ne saboda muna son mu bayar da muhimmanci ga kayan da muka sarrafa a Afirka."

Najeriya da ke zaman kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar dai taki sanya hannu kan wannan yarjejeniya, tana mai cewa za ta kula da nata kasuwancin da kamfanoninta da kanta.