1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kashin farko na alluran rigakafin kyandar biri ya isa DRC

September 5, 2024

Hukumomin kiwon lafiya na ganin alluran za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar mai baraza ga lafiya a duniya.

https://p.dw.com/p/4kJgd
Rigakafin kyandar biri a DRC
Rigakafin kyandar biri a DRCHoto: WHO/Aton Chile/IMAGO

A ranar Alhamis Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta karbi kason farko na alluran rigakafin cutar kyandar biri.

Hukumomin lafiya na ganin alluran za su taimaka wajen rage yaduwar cutar da ta tilasta wa Majalisar Dinkin Duniya ayyanata a matsayin barazana ga lafiya.

Najeriya za ta fara rigakafin kyandar biri cikin Oktoba

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta kasance kasar da annobar ta fi kamari kuma ta yadu zuwa kasashe makwabta da kuma sauran sassan duniya.

Rashin alluran rigakafin a kasar ya haifar da tsaiko wajen dakile yaduwar cutar a tsakanin al'umma.

Kyandar biri: AU ta ce annobar na karuwa a Afrika

Kasar ta kasance wacce cutar ta fi dagula wa lissafi sakamakon jinkirin da aka samu na isan alluran.