Kashi na 51 – Wasikar yabo ga Jan | Radio D Teil 2 | DW | 18.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 51 – Wasikar yabo ga Jan

Yanzu ya kamata mu sake yin ban-kwana: Kash! Aikin Jan ya kusa karewa, Philipp da Paula kuma suna tunanin wasikar yabo. Yau Jan ya nuna godiyarsa.

Akwai wata kwarya-kwaryar walima ta taya Jan murnar kammala zaman koyon aiki a Radio D. Ya yi wa abokan aikinsa ba-zata da ya ba su lemo da kayan lashe-lashe. Amma su Paula da Philipp suna ta fama rubuta masa wasikar yabo. Don haka, dole ne su yi amfani da kalaman da suka dace, saboda idan Jan ya sami kyakkyawan yabo, to, wannan zai sa ya sami shiga makarantar koyon aikin jarida.
Farfesa yana nazarin kalmomin mahadi na "falls" da "wenn", ya kuma yi wa masu saurare bayanin jumloli masu dauke da sharadi.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa