Kashi na 48 – Gabas da Yamma | Radio D Teil 2 | DW | 18.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 48 – Gabas da Yamma

A halin yanzu a ofishin Radio D, Paula tana nazarin sake hadewar Jamus. Ta gayyaci baki da yawa don su tattauna abin tare.

Paula tana gabatar da shiri mai taken "Jamusawan Gabas da na Yamma". Ta yi magana a kan wani dan Jamus ta Gabas makanike, da masanin halayyar dan adam, da wani kwararre a kan tattalin arziki. Wadannan sune tambayoyin da ta yi wa bakin a yau: Har yanzu akwai korafe-korafe? Wacce mahanga ta ci gaba ake da ita kuma tsakanin Jamusawan Yamma da na Gabas?
Farfesa ma yana da wadansu tambayoyi masu tsauri da zai amsa: yana karin haske a kan wanin lokaci na kalmomin aikatau na “haben” da “sein” da kuma hada wanin lokaci da kalmar aikatau ta “würde”.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa