Kashi na 47 – Gina katanga | Radio D Teil 2 | DW | 18.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 47 – Gina katanga

A Berlin, Paula da Philipp da Josefine sun ziyarci Reichstag, da Kofar Brandenburg, da "kwararon katanga" wanda ke nuna wurin da katangar take a da. Radio D sun gabatar da wasa a kan yadda aka gina katangar.

A yammacin ranar 13 ga Austan 1961, 'yan sandan Jamus ta Gabas suka fara gina katanga ta kan iyakar Jamus ta Yamma. Mutanen wani gida da yake daidai kan iyaka sai suka yanke shawarar su gudu. A Jamus ta Yamma kuma, 'yan kwana-kwana suka jira, suka kuma kama duk wanda ya diro ta taga.
A darasin nahawu na yau, muna da harafi mai fayyacewa na "ein" da wakilin suna "eins". Farfesa ya ja hankalinku game da kurakuren da ka iya biyo baya a irin wannan yanayin.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa