Kashi na 46 – Dabbobin ″bear″ na Berlin | Radio D Teil 2 | DW | 18.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Radio D Teil 2

Kashi na 46 – Dabbobin "bear" na Berlin

Hankalin Paula da Philipp ya karkata kan wani biki da ake a Berlin na baje kolin dabbobin "bear", wanda masu fasahar zane-zane daga kasashe fiye 120 suka shirya. A hirar da aka yi za ta fito da bayani kan biki.

Can kuma a Berlin, Paula da Philipp sun tafi cikin birni don ziyarar karin ilimi, tare da Josefine da kuma Jan. Ba abin da yake burge Josefine sai wannan baje koli, inda aka jera dabbobin "bear" na roba guda 120 suna kewaya duniya a matsayin alamar hakuri da juna. 'Yan jaridun sun gana da kakakin masu shirya wannan biki don jin bayani game da dabbobin "bear".
A yayin da biki ya dauke hankalin wasu a Berlin, shi kuwa Farfesa yana da aiki a gabansa. Yana nan yana bayanin yadda kalmar sifa take karewa, idan ta zo kafin suna. Wannan fa aiki ne ja.

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa